Yansandan a Katsina sun ayyana neman wani shugaban barayi ruwa a jallo

10

Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta kame sama da mutane 50 da take zargin barayi ne ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar, inda ta kuma ta ayyana wani garwuttaccen shugaban barayi, mai suna Adamu Aleiro Yankuzo, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.

Adamu Yankuzo a cewar ‘yansanda, ya jima yana kai hare-hare a jihoshin Katsina da Zamfara, tare da kitsa harin baya-bayan nan a kauyen Kadisau dake yankin karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, wanda ya jawo kisan sama da mutane 52.

A sanadiyyar hakan, rundunar tayi alkawarin bayar da ladan naira miliyan 5 a kansa, ga duk wanda ya bayar da bayanai masu muhimmanci da zasu jawo kama shi.

Kwamishinan ‘yansanda jihar, Sanusi Buba, wanda ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da sauran wadanda ake zargin da masu garkuwa da mutane, yace wanda ake zargin ya kashe mutane dayawa tare da sace daruruwan shanu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen + 6 =