Za a rantsar da Evariste Ndayishimiye a matsayin shugaban kasar Burundi

8

Za a rantsar da sabon zababben shugaban kasar Burundi, Evariste Ndayishimiye, a yau, watanni 2 kafin ranar da aka shirya rantsar da shi.

Bikin rantsuwar wanda aka jawo kusa, yazo ne bayan wanda zai gada, Pierre Nkurunziza ya rasu a makon da ya gabata.

Ndayishimiye tsohon shugaban kungiyar tawaye ne, kamar Nkurunziza.

Ya samu goyan bayan wanda zai gada, kuma an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, wanda ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Nkurunziza ya rasu yana da shekaru 55 a duniya a ranar 8 ga watan Yunin da muke ciki, bayan ya gamu da bugun zuciya. Amma akwai rahotannin da ba a tabbatar ba, dake cewa yana fama da cutar corona.

Bayan shekaru 15 akan karagar mulki, Nkurunziza na shirin sauka a watan Augusta.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

8 + 8 =