Buhari ya taya murna ga sabon shugaban kasar Burundi Ndayishimiye

8

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya murna ga Evariste Ndayishimiye bisa kama aiki a matsayin shugaban kasar Burundi.

An rantsar da Ndayishimiye jiya Alhamis a Babban Birnin Kasar, Gitega.

A wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya fitar, shugaban kasar ya kuma taya murna ga gwamnati da jama’ar Burundi bisa mika ragamar mulki zuwa gwamnatin demokradiyya lami lafiya, biyo bayan mutuwar bazata da tsohon shugaban kasar Pierre Nkurunziza yayi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × one =