Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin da yasa ba za a dawo da jigilar jiragen kasa yanzu ba

7

Ministan sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi, yace dukkan wanda bai kiyaye bin ka’idojin hukumar jiragen kasa ba, ba za a barshi ya shiga jirgin kasa ba idan sun dawo jigila.

Amaechi ya sanar da hakan a shafinsa na Tuwita.

Ya kuma ce jiragen kasan baza su motsa ba muddin fasinjoji basu kiyaye da dokokin kariya daga annobar corona ba.

An bayar da rahoton cewa hukumar jiragen kasa ta dakatar da jigilar jiragen kasa a kasarnan tun ranar 23 ga watan Maris.

Mataimakin daraktan hulda da jama’a na hukumar jiragen kasa, Mallam Yakub Mahmood, ya sanar da haka a madadin hukumar a Lagos.

Yace dakatarwar ta biyo bayan rahoton barkewar cutar corona.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 − 11 =