Gwamnatin tarayya zata yanke shawara akan dokar hana tafiye-tafiye tsakanin jihoshi sati mai zuwa

5

Kwamitin karta kwana na shugaban kasa kan cutar corona yace ya fara bibiyar tsare-tsaren dage dokar hana bulaguro tsakanin jihoshi.

Da yake jawabi a wajen taron manema labarai na kwamitin da ake gudanarwa kowace rana a Abuja, jagora na kasa na kwamitin, Dr. Sani Aliyu yace za a sake bude titunan bayan an dauki matakan kariya daga corona a dukkan tashoshin motar dake kasarnan.

Sani Aliyu ya sanar da hakan bayan shugaban kwamitin, Boss Mustapha ya sanar da cewa sati mai zuwa gwamnatin tarayya zata yanke shawara akan dokokin kulle, wadanda suka hada da dokar hana tafiye-tafiye tsakankanin jihoshi.

Jagoran yace ana bibiyar tsare-tsaren da karamar ministar sufuri, Gbemisola Saraki ta gabatar, kuma za a bude titunan da zarar komai ya daidaita.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

ten − seven =