Kungiyar Kwadago ta Kasa reshen Kano ta dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki 7 da ta shirya tafiya

3

Kungiyar Kwadago ta Kasa reshen jihar Kano ta dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki 7 da ta shirya tafiya a jihar bisa wasu bukatu da suka hada da rage albashin ma’aikata na watan Mayu.

Wata sanarwar hadin gwiwa tace an dauki matakin biyo bayan cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin jihar Kano da gamayyar kungiyoyin kwadago.

Rahotanni sun bayyana cewa karin wa’adin da kungiyoyin suka bawa gwamnatin jihar makon da ya gabata, yazo karshe jiya Litinin da dare, inda aka tsara tafiya yajin aikin gargadin yau Talata, da ace ba a cimma matsaya ba.

Sanarwar tace yarjejeniyar da aka cimma ta hada da aniyar gwamnatin ta mayar da kudaden albashin ma’aikatan da ta rage.

A cewar sanarwar, gwamnatin zata duba yiwuwar fara aiwatar da cikakken karin albashi da dokar mafi karancin albashin na naira dubu 30 ta kawo, da zarar an samu cigaba a kudaden shigar gwamnati.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

6 + six =