Gwamnatin Tarayya ta ware kudi naira biliyan 600 domin bayar da lamunin aikin gona

23
Sabo Nanono

Ministan aikin gona da raya karkara, Sabo Nanono, yace gwamnatin tarayya ta ware kudi naira biliyan 600 domin inganta baiwa manoma damar samun lamunin kudaden aikin gona a kasarnan.

Sabo Nanono yace kimanin manoma miliyan 2 da dubu 400 ake sa ran zasu amfana daga bashin wanda babu kudin ruwa a ciki, da aka tsara da nufin kara karfin gwiwar amfani da fasahar zamani wajen noman shinkafa da sauran amfanin gonar da ake sayarwa.

Ministan yayi jawabi a wajen kaddamar da shirin tallafawa noman shinkafa na daminar bana a kauyen Tofai dake yankin karamar hukumar Gabasawa ta jihar Kano.

Sabo Nanono yace shirin zai agazawa manoma wajen samun nasarar habaka yawan amfanin gona, dogara da kai da kuma yalwar abinci a kasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × four =