BUA zai kafa kamfanin simiti da na wutar lantarki a Adamawa

19

Kamfanin simitin BUA, daya daga cikin manyan kamfanonin siminti a Afirka ta Yamma ya shirya assasa wani katafaren kamfanin simiti da kamfanin samar da wutar lantarki a kananan hukumomin Guyuk da Lamurde na jihar Adamawa.

An sanar da haka lokacin da shugaban kamfanin BUA, Abdul-Samad Rabi’u, ya jagoranci tawagar manajojin kamfanin zuwa wata ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, a gidan gwamnati dake Yola.

Abdul-Samad Rabi’u yace binciken farko ya nuna cewa kananan hukumomin biyu suna da arzikin limestone mai inganci kuma kamfanin BUA a shirye yake ya zuba jari a jihar.

Ya kara da cewa kamfanin BUA zai yi amfani da fasahoshi na zamani wajen samar da wutar lantarki ga kamfanin da za a gina da kuma al’ummar Guyuk da Lamurde, kari bisa samar da ayyukan yi ga mutane kimanin dubu 8.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one + 12 =