Shugaba Keita na Mali ya rushe kotun kundin tsarin mulki daidai lokacin da ake fama da zanga-zanga

16

Shugaban Kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya sanar da rushe kotun kundin tsarin mulki a wani yunkuri na yayyafawa wutar rikici wuta wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 4 a wata zanga-zanga ranar Juma’a.

Shugaban kasar yace bazai lamunci irin wannan tashin hankali ba.

Kotun ta zama jigon kiki-kakar bayan ta soke sakamakon farko na zabukan yan majalisu a watan Maris.

Ana ta cigaba da kiraye-kirayen shugaban kasa Keita yayi murabus.

Yan adawa na damuwa kan yadda yake kula da rikicin yan ta’adda a Mali, da matsin tattalin arziki da kuma zabukan da ake takaddama akai.

Wata sabuwar gamayyyar yan adawa karkashin jagorancin wani malamin addini Mahmud Dikko, na cigaba da neman sake sauye-sauye, bayan tayi watsi da matakan da shugaban kasar ya dauka a baya, ciki har da kafa gwamnatin hadaka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 + 4 =