Gwamnatin Tarayya zata hana mutanen wasu kasashe damar shigowa Najeriya

7

Gwamnatin Tarayya tace zata hana mutanen wasu kasashe damar shigowa Najeriya domin tabbatar da tsaron lafiya a filayen jiragen sama da ma kasar baki daya.

Tace wannan karin daliline da yasa gwamnati bata amince da sake dawo da sufurin jiragen saman yan kasuwa na kasa da kasa ba, masu shiga ko fita daga Najeriya.

Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya sanar da haka a Abuja lokacin da yake jawabi a wajen taron manema labarai na kwamitin karta kwana na shugaban kasa kan cutar corona.

Ministan yace masu kamfanonin jiragen sama suna bukatar a bude sararin sufurin sama gabadaya domin jigila a cikin kasa ko kasa da kasa amma ana bawa tsaron lafiya muhimmanci kafin a dauki wannan mataki.

Ministan ya kuma bayyana cewa an karkasa jadawalin zirga-zirgar jiragen sama a cikin kasa domin a magance cunkoso a filayen jiragen sama.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × one =