Mayakan Boko Haram 602 sun fice daga kungiyar

18

Jumillar yan Boko Haram 602 ne suka sanar da ficewarsu daga kungiyar tare da shan rantsuwar yiwa gwamnatin tarayyar Najeriya biyayya.

Tsaffin mayakan wadanda suka kammala samun horon canja aqidah da gyaran halayya, sun dauki alaqawarin a sansanin Mallam Sidi dake yankin karamar hukumar Kwami ta jihar Gombe.

Sun sanar da ficewarsu daga kungiyar Boko Haram a gaban wani kwamitin shari’ah mai wakilai 11.

Da yake jawabi a wajen rantsuwar, jagoran shirin kawo zaman lafiya a yankin, Bamidele Shafa, yace halartar tubabbun mayakan a gaban kwamitin na shari’ah, shine babban abinda ake bukata kafin a sake shigar da su cikin al’umma.

A cewar Bamidele Shafa, tun farkon fara shirin a 2016, an shigar da mayaka 893 cikin sansanonin shirin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 − fourteen =