An samu tsohon Fira-Ministan Malaysia Najib Razak da laifi a dukkan zarge-zargen rashawar da ake masa

25

Wata kotu a Malaysia ta sami tsohon Firaiministan kasar Najib Razak da laifin amfani da mukaminsa ta hanyar da ba ta dace ba dangane da wata badakalar biliyoyin daloli da ake tuhumarsa da wawashewa daga wani asusu mallakin gwamnatin kasar.

Alkalin kotun ya kuma samu Najib Razak da hannu dumu-dumu kan wasu tuhume-tuhumen da suka jibanci cin hanci da rashawa da halatta kudaden haram da kuma zamba cikin aminci.

Najib Razak zai iya shafe shekara da shekaru daure a gidan yari, ko da yake ana sa ran zai ci gaba da walwala a waje har lokacin da za a kammala shari’a kan karar da zai daukaka.

Wannan shari’ar ita ce ta farko cikin jerin shari’u akalla guda uku da tsohon firaiministan ke fuskanta, wacce aka shafe wata goma sha shida ana yinta.

Cikin tuhumar da ake masa, masu shigar da kara sun ce ya karkatar da miliyoyin daloli zuwa ga wani asusun ajiyarsa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 4 =