Mutane 3 sun mutu, 6 sun jikkata bayan Boko Haram ta kai hari a Maidugurin jihar Borno

3

An kai wa Maiduguri babban birnin jihar Borno hare-hare inda aka tayar da abubuwa masu fashewa kamar yadda wadanda suka shaida lamarin suka tabbatar.

Ma’aikatan lafiya da suka isa wurin sun ce mutane uku sun rasa rayukansu kuma shida sun jikkata.

Mazauna birnin na tsakiyar shirye-shiryen bukukwan Sallah babba ne yayin da lamarin ya auku.

An sami rahotannin fashewar wasu abubuwan da ake kyautata zaton bama-bamai ne a cikin birnin da yammacin Alhamis.

Shugaban sashen samar da tsaro na hukumar bayar da agaji ta Jihar Borno, Bello Dambatta, ya ce an harbo wasu gurneti guda hudu daga wajen birnin, inda suka fada wurare daban-daban.

Mohammed Abubakar wanda ya gane wa idonsa lamarin ya shaida wa manema labarai cewa gurnetin sun fashe ne a wasu yankunan birnin da ke cike da jama’a daura da ofishin jami’an shige-da-fice a lokacin da yan kasuwa da mazauna birnin ke komawa gidajensu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nine + twenty =