Kotun korafin zabe ta soke zaben gwamnan jihar Bayelsa inda ta umarci a sake sabon zabe

2

Kotun korafin zaben jihar Bayelsa dake zama a Abuja a yau ta soke zaben gwamnan jihar, Duoye Diri.

Kotun mai alkalai biyar karkashin jagorancin Mohammed Sirajo, ta yanke hukuncin cewa zaben bai halatta ba, saboda rashin saka jam’iyyar ANDP tare da dan takararta, King George, a zaben gwamnan jihar na ranar goma sha shida ga watan Nuwambar bana.

Kotun korafin zaben ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta gudanar da zaben cike gurbi cikin kwanaki casa’in.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa a ranar goma sha biyar ga watan Augusta, kotun ta tabbatar da zaben Gwamna Diri tare da mataimakinsa, Sanata Lawrence.

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, yace zai daukaka kara a hukuncin yau na kotun korafin zaben gwamna dake zama a Abuja, wanda ya soke zabensa.

Douye Diri yace a saboda haka, ya umarci lauyoyinsa da su shirya muhimman takardu.

Yayi jawabi jim kadan bayan hukuncin kotun.

Diri, a wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Daniel Alabrah, ya fitar, yace yana da kwarin gwiwar cewa shi ke da nasara a karshe.

Gwamnan ya bukaci yan jam’iyyar PDP tare da magoya bayansa da kada su razana, kuma su cigaba da zama lafiya tare da kiyaye doka da oda.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 + 8 =