Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari ta dawo daga Dubai

25

Uwargidan Shugaban Kasa, Hajiya Aisha Buhari, ta dawo kasarnan daga Birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa, wata majiya mai nagarta, wacce ta nemi a sakaye sunanta, ta tabbatar da hakan ranar Asabar.

SkyDaily ta gano cewa ta dawo ne ita kadai, akasi bisa rahotannin kafafen yada labarai dake nuni da cewa tana tare da ‘yarta Hanan, wacce ake shirin bikin aurenta a ranar 4 ga watan Satumbar bana, a cikin Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Majiyar ta kuma yi watsi da rade-radin cewa jirgin saman da ya kawo uwargidan shugaban kasar ya samu tangarda, inda majiyar tace babu abinda ya samu jirgin.

Ana da yakinin cewa uwargidan shugaban kasar ta yi tafiya zuwa Dubai domin a duba lafiyarta.

Hajiya Aisha Buhari ta bar kasarnan zuwa Dubai lokacin bukukuwan Sallah Babba, lamarin da ya rura wutar zargin cewa tana fama da rashin lafiya sosai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × 5 =