Amnesty International tayi kiran a kawo karshen hare-haren da ake kaiwa yan jarida a Najeriya

9

Kungiyar Amnesty International tayi kiran a kawo karshen yawan hare-haren da ake kaiwa gidajen yada labarai da yan jarida a Najeriya.

Kungiyar, mai fafutukar kare hakkin bil’adama, tayi kiran lokacin da take Allah wadai da zagin da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya yiwa wakilin jaridar Daily Trust, Eyo Charles.

A rawaito yadda Charles yayi sa’insa mara dadi tare da Fani-Kayode a wajen wani taron manema labarai.

Wani faifan bidiyon da ake yadawa ta manhajar WhatsApp ya nuna yadda Fani-Kayode ya fice daga wajen taron bayan ya zazzagi Charles, wanda yayi ikirarin cewa yayi masa tambayar cin mutunci.

Lamarin ya auku ranar Alhamis a wani hotel mai zaman kansa, inda tsohon ministan ke jawabi ga manema labarai dangane da zagayen da yake yi na duba ayyuka a jihoshin Kudu maso Kudu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × 2 =