Majalisar Kasa ta dage ranar dawowa daga hutunta

17

Majalisar Kasa ta sanar da dage ranar dawowarta daga hutu wanda aka shirya a ranar 15 ga watan Satumbar bana, zuwa ranar 29 ga watan Satumbar bana.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mukaddashin akawun Majalisa, Ojo Amos, ya fitar, wacce SkyDaily ta samu jiya Juma’a.

Ga abinda sanarwar tace a rubuce: “Ana sanar da Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai cewa dawowa zaman majalisar wanda aka shirya a ranar Talata 15 ga watan Satumbar 2020, an daga shi zuwa ranar Talata, 29 ga watan Satumbar 2020. Muna masu nadamar rashin jin dadin da canjin ranar ka iya jawowa.”

Yan majalisar sun tafi hutun shekara a watan Yuli, wanda aka yi nufin zai kwashe makonni takwas.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

16 − 6 =