An kori shugaban jam’iyyar APC na jihar Jigawa daga jam’iyyar

61

Kwamitin zartarwa na jamiyyar APC na mazabar Sara a karamar hukumar Gwaram ya kori dakataccen shugaban jamiyyar APC na jihar Jigawa, Habibu Sara, daga cikin jamiyyar.

Hakan ya biyo bayan rahoton kwamitin da shugabannin jam’iyyar na mazabar suka kafa domin bincike akan zarge-zargen rashin biyayya da ake masa, inda rahoton ya tabbatar da zarge-zargen.

Shugaban jamiyyar APC na mazabar Sara, Yusif Danbarno ya sanar da korar dakataccen shugaban jam’iyyar wanda yace a baya yaki amsa gayyatar da aka yi masa domin sasantawa.

Danbarno yace za a mika hukuncin ofishin jam’iyyar na mazaba na korar dakataccen shugaban zuwa ga ofishin jam’iyyar na karamar hukuma.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × one =