Gamayyar jam’iyyun adawa sun shirya karade Najeriya da zanga-zanga bisa karin kudin man fetur

14

Gamayyar Jam’iyyun Adawa tace ta shirya tsaf domin gudanar da zanga-zangar gama gari akan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gamayyar tace ta jawo hankalin kungiyoyin fararen hula da su bi sahun kungiyoyin kwadago wajen shiga zanga-zangar dangane da karin farashin man fetur da kudin wuta na baya-bayan nan.

Gamayyar wacce ta hada dukkan jam’iyyu da kungiyoyin siyasa a Najeriya, ta fadi haka cikin wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren ta, Chief Willy Ezugwu, wacce aka rabawa manema labarai.

Tace lokaci yayi da zata gayawa gwamnatin tarayya cewa hakurin mutane ya kare, bayan zuba idon da suka yiwa gwamnati mai ci tsawon shekaru biyar.

Gamayyar ta dage kan cewa a yanzu gwamnatin tarayya ta raina yan Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seventeen − 15 =