Tsohon shugaban kasar Mali Moussa Traoré ya rasu

18

Tsohon shugaban Mali, Moussa Traoré, ya mutu a gidansa dake Bamako, babban birnin kasar.

Ya rasu yana da shekaru 83 a duniya.

Traoré ya karbi mulki bayan wani juyin mulki a shekarar 1968 kuma ya cigaba da zama a matsayin shugaban kasar har zuwa lokacin da sojoji suka hambarar da shi a shekarar 1991.

Ya rike matsayin dattijo mai fada aji cikin yan shekarun da suka gabata, inda yake bayar da shawarwari ga matasan yan siyasar Mali.

Mutuwarsa ta dace da lokacin juyin mulkin Mali na 4, tun bayan samun yancin kai.

A watan da ya gabata, sojoji suka hambarar da shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita, biyo bayan makonni na zanga-zangar yan adawa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × 3 =