El-Rufa’i ya sanya hannu akan dokar da ta bayar da dama a dandake masu fyade

15

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya rattaba hannu a dokar hukunci mai tsanani kan duk wanda a ka kama da laifin fyade.

Dokar ta ba da damar kisa ko yin dandaka ga duk wanda a ka kama ya yiwa kananan yara ‘yan kasa da shekaru sha hudu fyade.

Hakama karkashin dokar za a iya yankewa masu laifin musu hukuncin daurin rai-da-rai.

Idan a ka kama mace kuwa, dokar ta ce za a cire mata wani sashe na al’aura da ake kira Fallopian Tube ko kuma a kashe ta.

Hakan yazo ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Muyiwa Adekeye, ya fitar a Kaduna.

Kazalika, duk baligin da a ka kama da laifin yiwa ‘yan kasa da shekara 14 fyade, za a saka sunan shi a kundin rajistar wadanda suka aikata fyade tare da wallafa su a kafafen yada labarai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight − 5 =