Sama da fursunoni 200 ne suka tsere daga gidan yari a Uganda

6

Sama da fursunoni 200 ne suka tsere daga wani gidan yari a garin Moroto da ke arewa maso yammacin kasar Uganda.

An bayyana cewa fursunonin sun gudu da bindigogi 15 da harsasai masu yawa.

Fursunonin sun harbe wani soja wanda ya yi yunkurin tare su.

Tuni dai jami’an gidan yari da kuma sojojin kasar suka kaddamar da wani shiri na musamman domin gano su.

Mai magana da yawun sojin kasar ya bayyana cewa har kawo lokacin hada wannan rahoton, sojojin suna bata kashi da fursunonin.

Ya kara da cewa an kama fursunoni biyu an kuma kashe daya.

An gina gidan yari a kasan tsaunin Moroto dake kusa da garin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 − four =