Kwamitin rabon arzikin kasa ya raba naira biliyan 676 da miliyan 410 ga gwamnatin tarayya da jihoshi da kananan hukumomi

19

Kwamitin rabon arzikin kasa a watan Augusta ya raba naira biliyan 676 da miliyan 410 ga gwamnatin tarayya da jihoshi da kananan hukumomin, a matsayin kudaden da aka samu a watan Yuli.

Bayanan rabon na kunshe cikin rahoton baya-bayan nan na kwamitin wanda hukumar kididdiga ta kasa ta saki.

A cewar rahoton, gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 273 da miliyan 190, jihoshi 36 sun samu jumillar naira biliyan 190 da miliyan 850, yayin da kananan hukumomi suka samu naira biliyan 142 da miliyan 760.

Rahoton ya kuma nuna cewa an raba naira biliyan 42 da miliyan 850 ga jihoshin masu arzikin man fetur a matsayin kashi 13 cikin 100 na hakar mai.

Jumillar kudaden da aka raba sun hada da naira biliyan 543 da miliyan 70 daga asusun tara kudade na kasa da kuma naira biliyan 132 da miliyan 620 na kudaden haraji na VAT.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 + 17 =