Zanga-Zanga: Gwamnonin Najeriya sun gana akan karin farashin mai da kudin wuta

19

Gabannin zanga-zangar gama gari da kungiyar kwadago ta kasa ta shirya gudanarwa a ranar Litinin domin adawa da karin farashin man fetur da kudin wuta, gwamnonin jihoshi sun gudanar da zaman ganawar gaggawa a yunkurinsu na hana aukuwar zanga-zangar.

Sakateriyar kungiyon gwamnonin ta kasa a cikin wata sanarwa da kakakinta, Abdulraz Bello Barkindo, ya fitar, tace ganawar ta yanar gizo ta fara da misalin karfe 6 na yamma.

Bello Barkindo yace kungiyar a wajen ganawar tayi kokarin shiga tsakani a rikicin dake tsakanin gwamnatin tarayya da gamayyar kungiyoyin kwadago.

Biyo bayan karin farashin sari na kudin mai zuwa sama da naira 160 kowace lita da kuma karin kudin wuta fiye da ninki, kungiyar kwadago ta kasa NLC tayi barazanar kiran zanga-zangar gama gari, muddin gwamnatin tarayya taki amincewa ta janye karin kudaden.

Kungiyar tace za a gudanar da zanga-zangar a fadin kasarnan a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight + eight =