Kotu ta umarci a ci gaba da shari’ar Ibrahim Zakzaky

30
Ibrahim El-Zakzaky

Wata babbar kotu a Jihar Kaduna ta umarci a ci gaba da shari’ar da aka kawo gabanta kan jagoran mabiya Shi’a a kasar, Sheik Ibrahim Zakzaky.

BBC Hausa ta ruwaito cewa Sheikh Zakzaky da matarsa Zeenatu na rike tun a shekara ta 2015 bayan mutuwar mabiyan sama da 300 a wata arangama da jami’an tsaro a garin Zaria.

Sojoji sun ce sun bude wa mabiyan wuta ne a matsayin martani bayan sun yi kokarin kai wa ayarin motocin babban hafsan sojin kasar hari.

A shekara ta 2019 aka haramta kungiyar bayan shafe tsawon watanni na zanga-zanga da rikici da jami’an tsaro

Lauyan Zakzaky, Mr Femi Falana ya bukaci kotun tayi watsi da tuhumar da ake wa shugaban ‘yan shi’ar.

Sai dai alkali kotun ya ce hakan ba mai yiwuwa ba ne saboda bai gama sauraron gundarin karar da aka shigar ba balantana ya yanke hukunci.

Sannan Elzakzaky bai amsa tuhume-tuhumen da ake masa ba.

Elzakzaky da matarsa sun musanta zarge-zargen da ake musu.

Alkalin dai ya tsayar da Nuwamba a matsayin watan ci gaba da sauraron karar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × three =