Osinbajo ya bukaci shugabannin kasashen da ake ajiya da su dawo da kudaden sata

14

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya bukaci shugabannin kasashen da ake ajiya, da su dage kan dawo da kudaden sata.

Kakakin Osinbajo, Laolu Akande, a wata sanarwa ranar Litinin a Abuja, yace mataimakin shugaban kasar ya sanar da haka a wajen kaddamar da wata mujalla wacce taron majalisar dinkin duniya akan cinikayya da cigaba ta wallafa dangane da illar safarar kudaden sata akan cigaban Nahiyar Afrika wanda aka gudanar ta bidiyon kai tsaye.

Osinbajo yace wani karin abu mai muhimmanci da ya kamata a lura da shi shine dawo da kudaden sata zuwa kasashen da aka sata, zai zama izina ga yan baya kuma ya karya gwiwar safarar dukiyar haram.

A cewarsa, tona asirin wadanda ke da hannu wajen safarar kudaden satar tare da kwato kudaden zai zama darasi sosai ga wadanda ke aika-aikar tare da karfafawa yan kasa gwiwa da kuma gyara barnar da hakan ya haifar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five + thirteen =