Gwamna El-Rufa’i ya gabatar da kasafin kudin badi na N237.52bn ga Majalisar Kaduna

6

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya gabatar da kasafin kudin badi ga Majalisar Dokokin Jihar Kaduna na naira biliyan 237 da miliyan 520.

Gwamnan wanda ya halarci zauren majalisar tare da mataimakiyarsa Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, ya ce an ware naira biliyan 124 wanda ya ce ya kai kusan kashi 79 cikin 100 na kasafin ga tattalin arziki da walwalar al’umma.

Gwamnan ya kara da cewa an saka kudin ne saboda tabbatar da cigaba da zuba jari a bangaren ilimi da harkokin lafiya tare da cigaba da aiwatar da shirin gwamnati na zamanantar da birane. El-Rufai ya kara da cewa an ware naira biliyan 157 da miliyan 560 ga manyan ayyuka, yayin da biliyan 79 da miliyan 960 za su tafi ga ayyukan yau da kullum.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × 1 =