Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 36 tare da raba mutane 470 da gidajensu

8

Akalla mutane 36 ne suka mutu yayin da wasu 470 suka rasa muhallansu biyo bayan ambaliyar ruwa wacce mamakon ruwan sama ya haifar a sassa daban-daban na jihar Sokoto daga watan Janairu zuwa yanzu.

Daraktan wayar da kai na hukumar agajin gaggawa ta jihar Sokoto, Mustapha Umar, ya sanar da haka a wani taron ganawa akan kula da annoba jiya a Sokoto.

Hukumar agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ce ta shirya taron ganawar.

Mustapha Umar yace kimanin hekta dubu 302 da 500 na gonaki ne suka nutse kuma kimanin dabbobi 120 ne suka mutu sanadiyyar ambaliyar ruwan da aka fuskanta a fadin jihar.

Yace kananan hukumomi 19 daga cikin 23 na jihar Sokoto ambaliyar ruwan ta shafa tun bayan fara damunar bana.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × 5 =