Yansanda a Katsina sun gabatar da mutane 23 da ake zargi da hare-hare, fashi da mamaki da sata

7

Hukumar yan sandan jihar katsina ta sanar da damke wasu mutane dake zargi akalla 23 wadanda ake zargi da aikata laifuffuka wanda suka hada da hare hare da garkuwa da mutane gami da sata.

Daga cikin wadanda ake zargin akwai Sani Haruna dan sheru 20 daga kauyen Kwakwara dake karamar hukumar Safana a jihar.

Sani Haruna ya amince cewa shi da wasu mutane 7 da suka tsere, sun kai hari a kauyen Kwakwara inda suka kashe wani mutun mai shekaru 60 mai suna Malam Murnai, da raunata dansa Gambo Sa’idu, kafin su tsere da shanaye 8 da tumaki 50 da kuma akuyoyi 10.

Wani daban da ake zargin mai shekaru 25 mai suna Sanusi Abubakar, dan kauyen Unguwar Gajere dake karamar hukumar Kankara a jihar shima an gabatar da shi.

Ana zargin Sanusi Abubakar ya hada kai da wasu mutane biyu da suka tsere wajen yin garkuwa da wani mai suna Huruna Garba wanda iyalansa suka biya naira miliyan 3 amatsayin kudin fansa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen + fifteen =