Shugaban Sojojin Kasa Tukur Buratai yayi zargin ana kitsa yadda za’a tarwatsa zaman lafiyar Najeriya

7

Shugaban Sojojin Kasa, Laftanal Janar Tukur Burutai yayi gargadin cewa sojoji baza su kyale bata gari su tarwatsa zaman lafiyar Najeriya ba.

Mukaddashin daraktan hulda da jama’a na hukumar soji, Kanal Sagir Musa, yace Buratai ya fadi hakan a jiya yayin zaman ganawa da manyan jami’an soji da kwamandojin barikoki da na filin yaki, wanda aka gudanar a Abuja.

Sagir Musa ya yiwa yan jarida jawabi akan abin da aka tattauna a zaman ganawar, lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Tukur Buratai ya gayawa manyan jami’an soji da kwamandojin barikoki da na filin yaki cewa babu hurumin rashin biyayya tsakankanin dukkan jami’ai da sojojin Najeriya.

Ya bayar da umarnin cewa dole su jaddadawa na kasa da su cewa hukumar soji ta jajirce wajen tabbatar da dorewar mulkin demokradiyya a Najeriya, kasancewar ita ce hanya daya tilo wajen samar da cigaba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × 5 =