An rushe masallatai bayan wasu yan daba sun kai hari kan Musulmai a jihar Enugu

39

Jami’an tsaro na aiki domin dawo da zaman lafiya bayan wasu yan ta’adda sun kai hari kan al’ummar musulmai a wasu bangarorin garin Nsukka na jihar Enugu.

Ance hatsaniyar ta fara lokacin da wata musulma dake sayar da tumatir ta dauki hayar Keke Napep daga kasuwar wani kauye zuwa shagonta dake garin, kuma takaddama ta kaure tsakaninta da mai keke napep akan kudin da zata biya.

An bayar da rahoton cewa jayayyar ta haifar da lalata tare da kona dukiyoyin musulmai a garin, wanda mazauna garin suka yi, daga baya kuma lamarin ya munana inda ya kai ga an kone masallatai biyu a garin.

Amma da aka nemi jin ta bakinsa, kakakin yansanda na jihar, ASP Daniel Ndukwe, yace hukumar yasanda bata da masaniya dangane da harin amma yayi alkawarin za a bincika.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight + six =