Gwamnatin Tarayya zata raba naira biliyan 5 domin ceto bangaren sufurin jiragen sama

7

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, yace kwanannan gwamnatin tarayya zata fara rabon kudin ceto na naira biliyan 5, wanda ta amince a bawa masu harkar sufurin jiragen sama.

Hadi Sirika ya sanar da haka a wajen bude taron jin bahasin jama’a na kwanaki 3 akan kudirori 6 na majalisar zartarwa da aka kirkira da nufin fasalin hukumomin kula da sufurin jiragen sama a kasarnan.

Yace masu kamfanonin jiragen sama zasu samu naira biliyan 4 yayinda sauran masu kasuwancin bangaren sufurin jiragen sama za a basu naira billiyan 1.

Sai dai, majalisar dattawa tace kudaden baza su isa ba, wajen tabbatar da dorewar masu harkar sufurin jiragen sama.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 − nine =