Mutane 25 sun mutu bayan wasu yan bindiga sun kai hari a Jami’ar Kabul a Afghanistan

4

Wani hari da aka kai kan jami’ar Kabul a Afghanistan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 25.

Wasu da dama kuma sun ji rauni a cewar majiyoyin tsaro da jami’ain gwamnatin Afighanistan.

An shafe tsawon sa’oi ana musayar wuta tsakanin dakarun Afghanistan da yan bindigar da suka mamaye makarantar yau Litinin.

Wani da abin ya faru kan idonsa ya ce maharan sun bude wuta kan dalibai har da masu neman tsira.

Tuni Kungiyar Taliban ta musanta hannu a harin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 − 3 =