#EndSARS: Kisan yansanda zalunci ne – El’Rufa’i

7

Gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna ya bayyana kisan yansanda da masu zanga-zanga suka yi a wasu sassan kasarnan da zalunci.

El-Rufa’i, wanda ya zanta da manema labarai ranar Litinin a Kaduna bayan zaman ganawar kungiyar gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya da sauran manyan masu ruwa da tsaki a yankin, yace dole a marawa yansanda baya wajen gudanar da ayyukansu.

Yace Sufeto Janar na Yansanda, Mohammed Adamu, yayi jawabi a zaman ganawar dangane da zanga-zangar EndSARS da abubuwan da ta haifar.

Gwamnan yace kungiyar tana goyon bayan yansanda kuma tayi amannar cewa za a iya samun bara gurbi a yansanda, kamar yadda ake samu a kowace hukuma.

El-Rufa’i yace kungiyar ta amince akan samar da yansandan cikin al’umma.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − 6 =