Mummunar girgizar kasa ta kashe mutane 100 a Turkiya

8

Yawan wadanda mummunar girgizar kasa ta kashe a yammacin Turkiya ya karu zuwa 100 a safiyar yau, a cewar hukumar kula da annoba ta kasar.

Girgizar mai karfin maki 7 ta kuma raunata mutane 994, a cewar hukumar, har yanzu akwai mutane 147 a asibitoci.

Hukuma ta kara da cewa ma’aikatan ceto na cigaba da kokarin zakulo mutanen da aka rasa wadanda ba a san adadinsu ba, a cikin gine-gine guda 5.

An yi murna tare da jimami a jiya bayan an ceto wata yarinya yar shekara 3 tare da wani matashi mai shekaru 14, daga cikin baraguzan gine-ginen da suka rushe.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − 1 =