Gwamnatin Tarayya na neman ciyo bashin Naira Biliyan 459 na aikin gona daga Brazil

7

Gwamnatin tarayya na neman amincewa domin ciyo bashin kudi Dala biliyan 1 da miliyan 200, kwatankwacin naira biliyan 459, domin aikin gona, daga gwamnatin kasar Brazil.

Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, ta sanar da haka a jiya lokacin da ta bayyana a gaban kwamitin kudi na majalisar wakilai domin kare kasafin kudin ma’aikatar ta.

Tace gwamnati ta aika da bukatar ciyo bashin zuwa ga majalisar kasa.

A cewarta, za a ciyo bashin da nufin magance matsalolin da ake msamu a bangaren aikin gona.

Tace gwamnati na shirin samar da fili kadada 100 a dukkanin jihoshi 36 domin noman abinchi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × five =