Gwamnatin Kano tana kashe sama da biliyan 4 wajen ciyar da yan bodin

27

Gwamnatin Jihar Kano tace tana kashe kudi sama da naira biliyan 4 da miliyan 600 a kowace shekara domin ciyar da daliban makarantun kwana su dubu 50 a jihar.

Kwamishinan ilimi na jihar, Sanusi Muhammad Kiru, ya sanar da haka a Kano domin cika shekara guda da samun mukaminsa, inda ya kara da cewa majalisar zartarwa ta amince da sake bibiyar kudin ciyar da daliban ga yan kwangilar, saboda hauhawar farashin kayan abinci.

A cewar Sanusi Kiru, gwamnati mai ci tana kuma kashe naira miliyan 93 wajen ciyar daliban Kano a wata Makaranta dake Niamey a Jamhuriyar Nijar, kazalika za a kashe naira miliyan 107 ga daliban da zasu koma makaranta kwanannan.

Kwamishinan ya kuma ce za a fara karatu a sabbin manyan makarantun hadaka guda 5 dake masaratun jihar Kano 5, a watan janairun badi, da dalibai 303 a kowace makaranta.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − 2 =