Ndume: Tsohon Dan Boko Haram ne yake da alhakin kisan Kanal Bako

14

Sanata Ali Ndume daga jihar Borno yayi zargin cewa wani tubabben dan Boko Haram ne yake da alhakin kisan wani Kanal na Soja, D.C Bako.

A cewarsa, tsohon dan Boko Haram din ya bawa yan Boko Haram bayanan shige da ficen sojan.

An kashe Kanal Bako a ranar 21 ga watan Satumba, a wani kwantan bauna da yan Boko Haram suka yi a kusa da Damboa, wani gari mai nisan kimanin kilomita 85 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ali Ndume, wanda shine shugaban kwamtin sojoji na majalisar dattawa, ya sanar da haka ga manema labarai a ranar Laraba, jim kadan bayan zaman kare kasafin kudin sojojin Najeriya.

Sanatan yana mayar da martani ne dangane da tambayoyin da ake masa akan samarwa da sojoji kudade, da kuma matsayar kwamitinsa dangane da mayar da tubabbun yan Boko Haram zuwa cikin al’umma, lamarin da yace ba daidai bane.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × two =