An kashe sojoji uku a wani harin kwantan bauna na yan Boko Haram a Borno

6

Akalla sojoji 3 da yan civilian JTF 2 aka kashe, inda aka raunata wasu a wani harin kwanton bauna da yan Boko Haram suka kaddamar ranar Asabar a kan wani ayarin motoci a garin Ja’alta dake kan hanyar Gajiram zuwa Monguno a jihar Borno..

Ayarin motocin ya hada da sojoji da yan civilian JTF, wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa sansaninsu dake Baga a yankin karamar hukumar Kukawa, sa’ilin da yan Boko Haram da yan ISWAP suka auka musu da hari a cikin motocin yaki 5.

Harin yazo awanni kadan bayan Gwamna Babagana Zulum ya ziyarci garin Baga a wata ziyarar aiki, inda ya tallafawa sabon matsugunni al’ummar Baga da kayan abinci.

Wani dan civilian JTF wanda ya tsira daga harin, ya shaidawa manema labarai cewa an gwabza kazamin fada tare da mayakan cikin sama da awa guda, kasancewar sojoji sun turo da karin jami’ai, inda aka kashe wasu daga cikin mayakan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 − three =