ASUU ta amince ta dakatar da yajin aiki kasancewar gwamnati zata biya N70bn

2

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa ASUU ta amince ta janye yajin aikin da take yi tsawon watanni 8, wanda ya tsayar da harkokin koyo da koyarwa a jami’o’in gwamnati tun daga watan Maris.

Shugabannin kungiyar sun cimma matsayar ranar Juma’a a Abuja, yayin wata ganawa tare da tawagar gwamnati karkashin jagorancin ministan kwadago da aikin yi, Dr Chris Ngige.

Gwamnatin ta kuma yi alkawarin biyan kudi naira biliyan 40 a matsayin alawus-alawus da kuma naira biliyan 30 domin gyaran tsarin ilimin jami’o’i, jumillar naira biliyan 70.

Gwamnatin tarayyar ta kuma amince da biyan cikon albashin malaman jami’o’in kafin ranar 31 ga watan Disamba.

Hakan na zuwa ne mako guda bayan gwamnatin tarayya ta amince da bukatar kungiyar ta ASUU na cire yayanta daga tsarin biyan albashi na bai daya, wanda ake kira da IPPIS.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × four =