Gwamnatin tarayya ta samar da shafin yanar gizo domin yan N-Power da aka fitar

23

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani shafin yanar gizo mai suna NEXIT domin masu cin gajiyar shirin Npower da aka fitar daga shirin, ‘yan rukunin A da B.

Ministar jin kai, Sadiya Umar Farouq, tace an samar da shafin tare da hadin gwiwar babban bankin kasa CBN, domin bawa wadanda aka fitar daga shirin na Npower, damar neman cin gajiyar shirye-shiryen samar da ayyuka daban-daban na gwamnatin tarayya.

Ministar ta sanar da haka cikin wata sanarwa da kakakinta, Nneka Anibeze, ya fitar ranar Juma’a.

Minsitar tace shafin na NEXIT zai duba cancantar wadanda suka ci gajiyar, domin dacewa da shirye-shiryen samar da ayyuka, a karkashin bakin na CBN.

Ta kara da cewa wadanda za su ci gajiyar, zai kasance sun cancanta bisa la’akari da matakan da bankin na CBN ya gindaya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seventeen − one =