Yanzu-Yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara ya sauya sheka zuwa PDP

66

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara Malam Ibrahim Wakkala ya fice daga jami’iyar APC zuwa PDP.

Wakkala Wanda shine mataimakin Abdulaziz Yari a karkashin jam’iyar APC na tsawon shekaru 8 daga shekarar 2011 zuwa 2019 ya bayyana ficewar tasa ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai yau a garin Gusau.

Tsohon mataimakin gwamnan yace ya yanke ficewa ne daga APC sakamakon rikicin dake damun jam’iyar a jihar Zamfara, da kuma halin ko in kula da jam’iyar ke nuna masu nakin tuntubarsu a dukkan Al’amurran da ya shafi jam’iyar.

Har ila yau, Wakkala ya shaida wa manema labarai cewa kafin komawarsa PDP, saida ya sanar da tsohon maigidansa Abdulaziz Yari da kuma uwar jam’iyarsa ta APC niyyarsa na sauya sheka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen − 14 =