Majalisar dattawa ta gayyaci ministan tsaro da wasu akan rashin tsaro

3

Majalisar Dattawa a yau Talata ta gayyaci ministan tsaro da hafsoshin soji tare da shugabannin hukumar yansanda da na DSS, dangane da halin rashin tsaron da ya ki ci, ya ki cinyewa a kasarnan.

Matakin ya biyo bayan kudirin da Sanata Bello Mandiya daga jiyar Katsina ya gabatar akan sace kimanin dalibai 330 na makarantar sakandiren kimiyya ta gwamnati dake Kankara a jihar, da aka yi kwanannan.

Majalisar ta dattawa ta kuma bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya aiwatar da rahoton kwamitin majalisar akan kalubalen tsaro, ba tare da wani jinkiri ba.

Yan majalisar ta dattawa a jawabinsu daban-daban dangane da kudirin, sun nuna rashin gamsuwarsu akan shugabannin hukumomin tsaro daban-daban a kasarnan, bisa gazawarsu wajen magance satar yaran da basu ji ba, basu gani ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 2 =