Majalisar wakilai ta dakatar da shirin gwamnatin tarayya na daukar ma’aikata dubu 774

20

Majalisar Wakilai ta nemi da a gaggauta dakatar da shirin gwamnatin tarayya na daukar ma’aikata na musamman, wanda ake cece kuce akai.

Majalisun kasa da ma’aikatar kwadago da aikin yi ta tarayya, sun yi karan batta dangane da daukar ma’aikata dubu 774 domin shirin.

A zaman majalisar na yau Talata, majalisar ta wakilai ta bukaci ma’aikatar kudi da kasafin kudi ta tarayya da kada ta samar da kudaden aiwatar da shirin.

Majalisar ta kuma soki tsigewar da aka yiwa darakta janar na hukumar sama da ayyukan yi ta kasa, Dr Nasiru Argungu, wanda yake goyon bayan yan majalisa a rikicin.

Majalisar ta kuma bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi mi’ara koma baya wajen mayar da Dr. Argungu kan mukaminsa.

Tuni karamin ministan kwadago da ayyukan yi, Festus Keyamo, ya nada wanda ya zai maye gurbin Dr. Argungu, bisa umarnin shugaban kasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 + 11 =