Gwamnatin Kano ta rufe Jami’ar Bayero da sauran manyan makarantu

8

Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Ganduje ya bayar da umarnin rufe jami’ar Bayero ta Kano da sauran manyan makarantun jihar, ba tare da bata lokaci ba.

Sanarwar tazo kasa da awanni 24 bayan gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati da masu zaman kansu a jihar.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba, dauke da sa hannun kwamishiniyar ma’aikatar ilimin gaba da sakandire, Dr. Mariya Bunkure, an shawarci dukkan daliban da su fice da cikin makarantun a yau.

Gwamnatin jihar ta kuma bukaci daliban da su cigaba da bibiyar litattafansu idan suna gida.

Sai dai, kwamishiniyar bata ce uffan ba dangane da dalilin rufewar, amma an gano cewa hakan bazai rasa nasaba da dawowar corona ba a kasarnan ko matsalar tsaro.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × two =