Shugaba Buhari ya bayar da umarnin sake bude iyakokin kasarnan

18
Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin gaggauta sake bude iyakokin kasarnan guda 4.

Fadar shugaban kasa ce ta sanar da haka ta shafin twitter a rana Laraba.

Gwamnatin tarayya a watan Augustan 2019 ta rufe iyakokinta na kasa domin dakile shigo da kwaya ta barauniyar hanya da kananan makamai da kayan abinci zuwa kasarnan, daga kasashen yammacin Afirka dake makotaka.

Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, tayi tsokacin bude iyakokin kasanrna a watan da ya gabata.

Zainab Ahmed tace kwamitin shugaban kasa da aka kafa dangane da lamarin ya kammala aikinsa, inda ya bayar da shawarar sake bude iyakokin. An sanar da bude iyakokin Seme da Ilella da Maigatari da Mfun a yau, yayin zaman majalisar zartarwa ta kasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − fifteen =