An fara rigakafin cutar corona a kasar Saudiyya

31

Saudiyya ta fara rigakafin cutar corona a ranar Alhamis, a cewar ma’aikatar lafiya, kwana daya bayan ta karbi jiragen ruwa dauke da alluran rigakafin.

Bidiyon da gidan talabijin na al-Ekhrabiya, ya nuna wani mutum da wata mace ana yi musu rigakafin a wata cibiyar lafiya dake Riyadh babban birnin kasar.

Jim kadan bayan haka, sai ministan lafiya, Tawfiq al-Rabiah, ya karbi nasa rigakafin.

Kasar ta Saudiyya ta karbi jiragen ruwa biyu dauke da alluran rigakafin a jiya, inda ta zama kasa ta farko data samu rigakafin.

Hukumomi sun bukaci mutane da suyi rijistar rigakafin ta wata manhajar waya da ma’aikatar ta samar.

Sama da mutane dubu 150 ne suka yi rijista cikin awanni 24.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

7 − three =