An samu adadi mafi yawa na wadanda suka kamu da Corona a rana guda a Najeriya

5

Ga dukkan alamu zagaye na biyu na annobar corona ya iso Najeriya, bayan kasar ta samu adadi mafi yawa na sabbin wadanda suka kamu da cutar a rana guda su 930 a ranar Laraba.

Tun bayan zuwan cutar a watan Disamba, ba a taba samun adadin wadanda suka kamu a rana guda sama da mutane 745 da aka samu a ranar 19 ga watan Juni.

Yawan mutanen da cutar ta hallaka a kasarnan suna tsaya a dubu 1 da 200, kasancewar babu rahoton wanda ya rasu a ranar Laraba.

Yawan wadanda ke jinyar cutar a kasarnan sun karu daga kimanin dubu 3 zuwa sama da dubu 5 saboda karuwar wadanda suka harbu.

Daga cikin jumillar mutane sama da dubu 75 da suka kamu da cutar a Najeriya, mutane dubu 66 sun warke an sallamesu daga asibitoci.

Hakan yazo ne daga bayanan da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta wallafa a jiya da dare.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight + 6 =