Pantami ya soke kudin ganin number shaidar dan kasa ta waya

0

Ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, ya umarci hukumar sadarwa ta kasa NCC da hukumar shaidar zaman dan kasa da su cire tarar naira 20 da aka kakaba akan masu masu amfani da waya wajen neman numbersu ta shaidar zaman dan kasa.

Sheikh Pantami ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakinsa, Uwa Suleiman, ta fitar a Abuja.

Umarnin na ministan, wanda mai magana da yawun nasa tace ya fara aiki nan take, dauki ne aka yi da nufin saukakawa da kuma rangwame.

Yace mataimakin shugaban hukumar sadarwa ta kasa da darakta janar na hukumar shaidar zaman dan kasa, sun sanar da shi cikin wata wasika dake dauke da fara aiwatar da umarnin, cewa hukumomin da abin ya shafa sun gana inda suka sanar da kamfanonin waya halin da ake ciki.

Tun a baya, gwamnatin tarayya ta umarci a hada shaidar zama dan kasa da layukan waya domin lamuran tsaro.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × one =