Fadar shugaban kasa zata hana makiyaya yawo saboda tsaro

42

Fadar shugaban Kasa ta bayyana cewa zata dakatar da Fulani makiyaya daga tafiye-tafiye a sassan kasar nan domin kiyaye fadace-fadace tsakanin Manoma da Makiyaya.

Babban Mai taimakawa shugaban Kasa kan kafofin Sadarwa Mallam Garba Shehu, shine ya bayyana hakan a yau, lokacin da ya bayyana a Gidan Talabijin na Channels Tv.

Garba Shehu, ya alakanta tafiye-tafiyen da Fulani sukeyi da Cinye Makiyaya da akayi a Sassan Arewacin Najeriya.

A cewarsa Kwararomar Hadama, na daya daga cikin abubawan da suke Cinye wuraren Kiwo a Arewacin Najeriya, wanda hakan ya tirsasawa Makiyaya zuwa Kudancin kasar nan domin neman Abincin da dabbobinsu zasu ci da kuma ruwan da zasu sha.

Kazalika, ya bayyana cewa gwamnonin Arewa ta Tsakiya suna gudanar da wasu shirye-shirye domin magance matsalar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

16 + fifteen =